15 Yuni 2026 - 08:28
Source: ABNA24
Shekh Zakzaky (H): Ceton Al'umma Ne Manufarmu - Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)  + Hotuna

Jagora (H) ya bayyana cewa ayyukan da sassa daban-daban na Harka Islamiyya ke gudanarwa na ceton al'umma ne, yayin da yake gabatar da jawabin rufe Mu'utamar na Dandalin Kiwon Lafiya (ISMA) karo na 28, yau Lahadi, 28 ga Zul Hijja 1447, a gidansa da ke Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Da yake bayani kan ayukkan ISMA, ya bayyana su a matsayin ayyuka masu matuƙar muhimmanci, wanda ya ce ayyuka ne na ceton rayuka. Haka kuma, ya yi tsokaci kan wasu ayyuka da Lajnonin Harka ke gudanarwa a fannoni daban-daban a cikin al'umma, wanda ya ce "duka dai ana aiki ɗaya ne, kula da al'umma." Ya ce ayyukanmu shaida ce ta kyakkyawar manufarmu ga al'umma, saɓanin yadda maƙiya ke ƙoƙarin nuna mu.

Sai dai, Jagora (H) ya nuna damuwa kan yawaitar shaye-shaye da illolin da yake haddasawarwa cikin al'umma. Ya ce, maƙiya na amfani da shi a matsayin makami don  lalata tarbiya, "makami ne shi ƙwaya; suna amfani da shi wurin lalata tarbiya da kuma sa matasa su aikata abin da suke so."

A ƙarshe, ya yi kira da ci gaba da ayyukan hidimtawa da ceton al'umma, tare da jaddada mahimmancin tallafawa irin waɗannan ayyukan. "A ci gaba da ayyukan hidimtawa al'umma tare da jajircewa da yin su don Allah."

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)28/DhulHijja/1447

14/06/2026

Your Comment

You are replying to: .
captcha